logo

HAUSA

Masanan Sin sun cimma nasarar shuka shinkafa dake nuna da sauri a yankin hamadar Xinjiang

2024-05-07 08:07:41 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, ina da wata tambaya, tsawon wane lokaci shinkafa ke kaiwa kafin ta nuna a Najeriya? Kwanan baya, a karon farko, an samu nasarar shuka shinkafa mai saurin nuna a cikin rumfar musamman da aka kafa a yankin Hotan, na jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya nuna nasarar da kasar Sin ta cimma a noman shinkafa a hamada.