Masar ta samu kyakkyawan martani daga Hamas da Isra’ila game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
2024-05-07 10:42:30 CMG Hausa
Tawagar tsaro ta kasar Masar, wadda ke shiga tsakani a batun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ta ce ta samu martani mai gamsarwa daga bangarorin Hamas da Isra’ila.
A jiya Litinin ne kafar watsa labarai ta Al-Qahera dake Masar, ta hakaito hakan daga wata majiyar tsaro mai tushe. Kafin hakan, kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta bayyana amincewarta da sharuddan tsagaita bude wuta da aka gabatar, wadanda ta ce sun dace da muradunta, ciki har da sake gina zirin, da mayar da mazauna yankunan da aka raba da matsugunansu gida, da musayar fursinoni da bangaren Isra’ila.
Har ila yau a dai jiyan, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila Daniel Hagari, ya ce Isra’ila tana nazari, da tantance kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta da Masar ta gabatar tun a baya wanda ya samu amincewar Hamas.
To sai dai kuma a daya bangaren, sojojin Isra’ila na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen kaddamar da hare-hare ta kasa a birnin Rafah na kudancin zirin Gaza, birnin da a halin yanzu ’yan gudun hijira kusan miliyan 1.2 ke samun mafaka a cikinsa. (Saminu Alhassan)