logo

HAUSA

Ziyarar Shugaba Xi a Turai ta kara bayyana muradin Sin na ganin tabbatuwar zaman lafiya a duniya

2024-05-07 18:41:57 CMG Hausa

Yayin da shugaban Sin Xi Jinping ke ci gaba da ziyara a kasar Faransa, ya tattauna da manema labarai tare da shugaban kasar Emmanuel Macron, a jiya Litinin. Shugaba Xi ya bayyana wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa, kuma daga cikinsu akwai wadanda suka fi jan hankalina su ne:

Na daya, a shirye Sin take ta hada hannu da Faransa wajen amfani da wasannin Olympics a matsayin dandali na wanzar da zaman lafiya a duniya. Ba sai an fada ba, duk mun san yanayi na hargitsi da duniya take ciki yanzu haka, kana mun san irin rawar da wasanni ke takawa wajen ingiza hadin kai da zaman lafiya tsakanin mabanbantan al’ummomi. Hakika kasar Sin ta yi kyakkyawan tunani na amfani da wasannin na duniya, wajen ingiza sulhu tsakanin kasa da kasa. Matasa su ne kashin bayan kowanne al’umma. Don haka, idan ana amfani da dandamali irin na Olympics wajen yayata bukatar zaman lafiya da kyawawan akidu, a nan gaba za a samu al’umma mai fahimta da ganin mutuncin juna, wadanda za su rayu cikin zaman lafiya.

Na biyu, Sin na goyon bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine. Tabbas kamar yadda shugaban ya fada, maimakon ingiza rikici ko tallafawa rikicin kamar yadda wasu ke yi, kasar Sin ta kasance mai kira da warware rikicin ta hanyar tattaunawa. Tarihi ya nuna cewa sulhu ba ya samuwa sai da tattaunawa, don haka ya dace bangarori masu ruwa da tsaki da ma wadanda ke ci gaba da ruruta wutar rikicin, su mayar da wuka kube, su rungumi mafita mafi dacewa ta hawan teburin sulhu domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Na uku, kasar Sin na kira da a dakatar da bude wuta a rikicin Palasdinu da Isra’ila tare da kafa kasashe biyu. Sanin kowa ne Sin ta kasance gaba gaba wajen kiraye-kirayen tsagaita bude wuta ga rikicin. A matsayinta na babbar kasa, har kullum tana goyon bayan samar da zaman lafiya a duniya, tare da kasancewar murya ga masu rauni. Dadewar da aka yi ana takkadama tsakanin bangarorin biyu ya tabbatar da cewa, idan ba samar da kasashe biyu aka yi ba, ba za a taba samun zaman lafiya ba, kuma rikici na iya bazuwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

A ganina, hadin gwiwa tsakanin Sin da Faransa, zai taka rawa wajen dakile fito na fito da wasu kasashe ke neman tadawa tsakaninsu da Sin, haka kuma zai dakile bullar kananan rukunonin da ake kafawa da zummar dakilewa ko matsawa wata kasa lamba. Ziyarar shugaban Sin a Turai, ta nuna cewa, Sin ba ta neman kafa rukunin kawaye, sai dai rugumar kowa da kowa domin inganta dunkulewar kasashen duniya, ba tare da wariya ba, domin samar da zaman lafiya mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)