logo

HAUSA

Sin za ta taimakawa Kenya da agajin jin kai da na sake gina sassan da ambaliya ta lalata gwargwadon karfin ta

2024-05-06 16:32:54 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yiwa al’ummar kasar Kenya ta’aziyyar mutane sama da 200 da suka rasu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta aukawa wasu sassan kasar a baya bayan nan.

Lin Jian, ya bayyana kaduwa bisa asarar da ambaliyar ta haifar, yayin da yake jagorantar taron manema labarai na yau Litinin, inda ya yi tsokaci kan tambayar da wani dan jarida ya yi masa don gane da ambaliyar ta kasar Kenya.

Ya ce kasar Sin za ta samar da tallafin shawon kan ibtila’in da ya auku a Kenya, da ma na taimakawa sake gina sassan da lamarin ya shafa gwargwadon karfin ta, kuma bisa la’akari da yanayin ibtila’in, da kuma bukatar bangaren Kenya. (Saminu Alhassan)