logo

HAUSA

Manzon musaman na shugaba Xi Jinping ya halarci taron koli na kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na 15

2024-05-06 10:45:21 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin Zheng Jianbang, ya halarci taron koli na kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na 15, wanda ya gudana tsakanin ranaikun 4 zuwa 5 ga wannan nan na Mayu a birnin Banjul, fadar mulkin kasar Gambia.

Yayin da yake halartar taron, Zheng Jianbang ya karanta sakon taya murnar budewa a madadin shugaba Xi Jinping na kasar Sin. Har ila yau, a jiya Lahadi 5 ga wata, shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya gana da Zheng Jianbang, inda wakilin na shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin da Gambia abokai ne na gari, kana Sin tana sada zumunta da kasashen musulmi. Ya ce a shekarun baya baya nan, an gaggauta raya dangantakar Sin da Gambia a dukkan fannoni. An kuma fadada imani da juna, da hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakanin kasashen biyu, wanda hakan ya amfani jama’arsu baki daya.

A nasa bangare, shugaba Barrow ya bayyana cewa, Sin ta samar da babbar gudummawa ga kasar Gambia, a fannonin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, yayin da kasar Gambia ke dora muhimmanci sosai kan sada zumunta tare da kasar Sin, da nuna goyon baya ga ka’idar Sin daya tak, kana tana fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a dukkan fannoni, don daga dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)