logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya wallafa bayaninsa a jaridar Faransa

2024-05-06 11:19:15 CMG Hausa

A jiya Lahadi, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake ziyara a kasar Faransa, ya wallafa wani bayani mai taken “Gadon akidar kulla hulda tsakanin kasashen Sin da Faransa, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a duniya” a jaridar Le Figaro ta kasar.

A cikin bayanin, shugaba Xi ya bayyana cewa, ziyararsa a kasar Faransa a wannan karo, ta shaida manufofin Sin guda uku. Na farko, Sin tana son yada akidar kulla hulda tsakanin kasashen Sin da Faransa, don sa kaimi ga ci gaba da raya dangantakarsu. Na biyu, Sin za ta kara bude kofa mai inganci ga kasashen duniya, da zurfafa hadin gwiwa tare da sassan kasa da kasa ciki har kasar Faransa. Na uku kuwa, Sin tana son kara yin mu’amala da hadin gwiwa tare da kasar Faransa, don tabbatar da zaman lafiya da karko a duniya baki daya.  (Zainab Zhang)