logo

HAUSA

’Yan kasar Chadi mazauna Najeriya sun yi fatan sabon shugaban kasar zai tabbatar da hadin kan al’ummar kasar Chadi baki daya

2024-05-06 16:45:49 CMG Hausa

Yau Litinin 6 ga wata, al’ummar kasar Chadi dake yankin Afrika ta tsakiya ke gudanar da zaben shugaban kasa a kasar a karon farko tun bayan rasuwar tsohon shugaba Idris Deby a 2021.

Zaben na yau Litinin za a fafata ne da dan tsohon shugaban kasar wato Mahamat Deby Ethno na jam’iyyar Patriotic Salvation Movement wanda dai shi ne yake rike da shugabancin kasar a yanzu haka, kamar dai yadda majalissar lura da harkokin zaben kasar ta bayyana an samar da lokacin zagaye na biyu na zaben idan har yanayi ya nuna hakan a ranar 22 ga watan Yunin 2024.

Zaben na yau shi ne zai kawo karshen gwamnatin mulkin soji zuwa na farar hula a kasar ta Chadi mai yawan al’umma miliyan 18.3 a tsididdgar da aka yi na 2023.

To ko mene ne fatan ’yan kasar ta Chadi mazauna Najeriya a game da sabon shugaban za a a zaba? Ga dai bayanin nasu a ganawarsu da wakilin sashen Hausa na CMG a Najeriya Garba Abdullahi Bagwai. 

“Suna na Mohammad Kubure dan Chadi mazaunin garin Najeriya. Yau Litinin za a yi zabe insha Allahu a garin mu na Chadi, sabo da haka ni shawara ta gare ku mutanen Chadi da bakin da ’yan garin gaba daya, mu bada hadin kai sosai wajen ganin cewa an yi wannan zabe lafiya, an waste lafiya.”

“Da farko dai ni suna na Muhammad Umar Adam Mattum dan Chadi mazaunin nan Najeriya, gaskiya fata na Allah ya zabar mana da shugaba mafi alheri wanda zai kula da talakawanmu zai kula mana da harkar tsaro da harkar lafiya da harkar nomanmu, kuma ina yiwa wannan gidan rediyo mai albarka ina musu fatan alheri kan irin namijin kokarin da suke yi.” (Garba Abdullahi Bagwai)