logo

HAUSA

An yi bikin mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Faransa

2024-05-06 21:10:44 CMG Hausa

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake ziyarar aiki a kasar Faransa, a yau Litinin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya bikin mu’amalar al’adu a birnin Paris, domin taya murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Faransa. Yayin bikin mai taken “Shekaru 60 masu kyau, Zumuncin Sin da Faransa”, an gabatar da fina-finai da shirye-shiryen talabijin masu kyau da kasar Sin da kasar Faransa suka tsara cikin hadin gwiwa. A sa’i daya kuma, an kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakanin CMG da Gidan talabijin na watsa labarai na Turai wato Euronews. (Maryam)