logo

HAUSA

Adadin tafiye tafiyen yawon bude ido na cikin kasa yayin hutun ranar ma’aikata na kasar Sin ya kai kusan miliyan 300

2024-05-06 15:39:58 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta fitar a Litinin din nan sun nuna cewa, adadin tafiye tafiye na yawon bude ido a cikin kasar da aka yi yayin hutun ranar ma’aikata a kasar Sin, ya kai kimanin miliyan 295.

Alkaluman sun shaida yadda wannan adadi ya karu, yayin kwanaki biyar na hutun da aka kammala a jiya Lahadi, da kaso 7.6 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara, da kuma karuwar kaso 28.2 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019. (Saminu Alhassan)