logo

HAUSA

Hada hadar cinikayya a fannin ikon mallakar fasahohi ta Sin ta bunkasa a shekarar bara

2024-05-06 09:38:27 CMG Hausa

Alkaluman hukumar lura da musaya da kasashen ketare ta kasar Sin, sun nuna yadda hada hadar cinikayya a fannin ikon mallakar fasahohi ta Sin ta bunkasa a shekarar 2023 da ta gabata, wanda hakan ke nuni ga yadda kasar ke kara samun kyautatuwar takara tsakanin ta da sauran sassan kasa da kasa a fannin.

Alkaluman sun nuna cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2023, matsakaicin darajar ci gaban kudaden da ake samu daga moriyar ikon mallakar fasaha ta kasar ta Sin a shekara guda ya kai kaso 9.4 bisa dari.

Kaza lika a shekarar bara kadai, jimillar hada hadar cinikayyar da aka yi a fannin cin riba daga ikon mallakar fasaha a kasar Sin, ta kai ta dala biliyan 53.7. Cikin jimillar, kudaden da aka samu bisa fitar da fasahohi zuwa ketare sun kai dala biliyan 11, adadin da ya karu da kusan kaso 70 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019.   (Saminu Alhassan)