Kasar Sin ta soki furucin jami’in Amurka dake cewa ana damawa da yankin Taiwan cikin tsarin MDD
2024-05-06 20:36:48 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya soki furucin da wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya yi cewa, ana damawa da Taiwan kamar yadda ya dace a tsarin MDD, yana mai bayyana hakan a matsayin jirkita gaskiya da tarihi da ma take ka’idojin dokokin duniya da na dangantakar kasa da kasa.
Lin Jian ya bayyana a yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum cewa, ba za a taba iya kalubalantar kudurin MDD mai lamba 2758 ba, kuma ba za a iya sauya manufar Sin daya tak ba. Ya ce tabbas goyon bayan ‘yancin Taiwan zai haifar da matukar bacin rai.
Kakakin ya kara da cewa, Sin na shawartar Amurka ta kasance tare da galibin kasashen duniya wajen tsayawa a bangaren da ya dace da yin biyayya ga shawarar da babban zauren MDD ya yanke, tare da goyon bayan manufar Sin daya tak da sanarwoyi 3 dake tsakanin Sin da Amurka da kuma biyayya ga alkawuran da shugabannin Amurkar suka yi na kin goyon bayan ‘yancin Taiwan ko kasashen Sin biyu, ko kasar Sin da kasar Taiwan, da sauran alkawura masu ruwa da tsaki da suka dauka, tare da dakatar da keta matsayar da Sin ta dauka kan Taiwan ta ko wacce hanya. (Fa’iza Mustapha)