Ana gabatar da shirin sada zumuntar tsawon shekaru 60 a kasar Faransa
2024-05-06 14:39:20 CMG Hausa
Tun daga jiya Lahadi aka fara gabatar da shirin bidiyo na “Sada Zumuntar Tsawon Shekaru 60”, a kafofin telebijin na sassa 8, wato na Turai, da na Asiya da tekun Pasifik, da na Afirka, da sauransu, ta tasha mai lamba 5 ta gidan telebijin na kasa da kasa na Faransa, cikin harsuna 13, da suka hada da Faransanci, da Turanci da sauransu.
Tashar sashen Turai ta babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da kafa ta 5 ta gidan telebijin na kasa da kasa na kasar Faransa, su ne suka yi hadin gwiwar daukar shirin cikin watanni 6, kana ana sa ran masu kallo na sassan duniya miliyan 400 za su kalli shirin.
A cikin shirin an zanta da shahararrun mutane fiye da 10, wadanda suka bayar da muhimmiyar gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa. Kaza lika shirin zai nuna yadda al’ummun Sin da na Faransa suke sada zumunta, da yin hadin gwiwa wajen samun ci gaba a cikin shekaru 60 da suka gabata. (Zainab Zhang)