logo

HAUSA

An gudanar da bikin tattaunawa a tsakanin matasan Sin da Faransa

2024-05-06 09:49:54 CMG Hausa

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasar Faransa, an gudanar da wani biki na tattaunawa a tsakanin matasan Sin da na Faransa, mai taken “Fahimtar zamanintarwa irin na kasar Sin” a birnin Paris dake kasar Faransa, wanda babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da kungiyar daliban da suka gama karatu a jami’ar siyasa ta Paris, da kwamitin harkokin jami’o’i na MDD na birnin Paris, da jami’ar Jinan ta kasar Sin suka yi hadin gwiwar karbar bakunci.

Shugaban gidan CMG Shen Haixiong, da tsohon ministan harkokin kasa da al’adu, da bada ilmi na kasar Faransa Jack Lang, da tsohon jakadan Faransa dake kasar Sin Sylvie Bermann, da masanin kwalejin kimiyya da fasaha na kasar Faransa Hervé Machenaud, da shugaban kwamitin harkokin jami’o’i na MDD na birnin Paris Charles Jeanne sun halarci bikin tare da bada jawabi.

Kaza lika yayin bikin, shugaban rukunin sada zumunta a tsakanin Faransa da Sin na majalisar dokokin jama’ar kasar Faransa Éric Alauzet, da memban rukunin sada zumunta a tsakanin Faransa da Sin na majalisar dattijai ta kasar Faransa Jean Hingray, tare da sauran mahalarta bikin sun kalli gabatarwar rahoton binciken zamanintarwa irin na kasar Sin, wanda matasan Sin da Faransa suka yi, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan batun zamanintarwa irin na kasar Sin, da kara yin imani da juna a tsakanin matasa, don kara kuzari ga sada zumunta a tsakanin Sin da Faransa. (Zainab Zhang)