logo

HAUSA

Yawan zirga-zirgar jiragen kasa da suka tashi daga gabashin kasar Sin zuwa kasashen Turai ya kai wani sabon matsayi

2024-05-05 16:54:40 CMG Hausa

Rahotanni sun bayyana cewa, ya zuwa ranar 5 ga watan Mayun bana, jimillar jiragen kasa 2,000 ne suka ratsa ta tashoshin jiragen kasa na Manzhouli, Suifenhe, da Tongjiang dake gabashin kasar Sin, zuwa kasashen Turai, wadanda suka yi jigilar kwatainonin kayayyaki 210,000, adadin da ya karu da kashi 7% da kashi 6% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara, wanda kuma aka cimma kasa da kwanaki 9 idan aka kwatanta da lokacin da aka dauka a shekarar da ta gabata, haka kuma, wannan adadi ya kafa wani sabon tarihi, tare da samar da ci gaba yadda ya kamata.

Tun daga farkon wannan shekara, yawan zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin da ke dakon kaya a tashoshin jiragen kasa na Manzhouli, Suifenhe, da Tongjiang ya kai kusan kashi daya bisa uku na jimillar adadin na kasar baki daya, kuma ana ci gaba da inganta zirga-zirgar kayayyaki tsakanin kasar da kasashen ketare.

A halin yanzu, ta hanyoyin jiragen kasa dake tashi daga tashoshin dake gabashin kasar Sin zuwa kasashen Turai da yawansu ya kai 24, ana iya zuwa kasashen Turai 14, wadanda suke ratsa birane sama da 60 na kasar ta Sin.

Kayayyakin da aka yi jigilar su sun kunshi manyan nau'ikan 12, wadanda suka hada da kayayyakin lantarki, da kayayyakin yau da kullum, da injinan masana'antu, da kayayyakin aikin gona da sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)