logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi jawabi bayan isa kasar Faransa

2024-05-05 22:27:04 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a rubuce bayan da ya isa birnin Paris na kasar Faransa a yau Lahadi, 5 ga wata, inda ya ce ya yi farin cikin fara ziyarar aiki karo na uku a Jamhuriyar Faransa.

A yayin ziyarar, zai yi musayar ra’ayi mai zurfi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, kan ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa da kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Turai karkashin sabon yanayin da ake ciki, da ma manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)