'Yan cirani a kasar Sin sun samu karin kudin shiga a 2023
2024-05-05 16:47:02 CMG Hausa
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce a shekarar 2023, 'yan cirani daga kauyukan kasar Sin sun more karin kudin shiga da kyakkyawan yanayin rayuwa.
A cewar rahoton da hukumar ta fitar, a shekarar 2023, abun da 'yan cirani ke samu a kowanne wata ya kai yuan 4,780 kwatankwacin dala 672.6 a matsakaicin mataki, karuwar kaso 3.6 a kan na shekarar 2022.
Haka kuma, fadin muhallin kowanne mutum a birane ya karu daga murabba'in mita 1.4 zuwa 24.
Har ila yau, rahoton ya ce a wannan shekarar, yawan 'yan ci ranin ya kai miliyan 297.53, karuwar miliyan 1.91 kan na shekarar 2022. (Fa'iza Mustapha)