logo

HAUSA

Wasu 'yan kasuwar kasar Sin sun isa jihar Kano domin saka jarin buliyoyin naira wajen gina kamfanin casar Shinkafa

2024-05-05 15:17:00 CMG Hausa

Wasu 'yan kasuwar kasar Sin sun isa jihar Kano dake arewacin Najeriya domin saka jari wajen kafa kamfanin sarrafa shinkafa da za a kasha buliyoyin naira.

A lokacin da yake jawabi bayan ya karbi bakuncin tawagar 'yan kasuwar a ofishin sa ranar juma'a 4 ga wata, kwamashinan ma'aikatar kasuwanci da masana'antu na jihar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ya ce, zuwan 'yan kasuwar na kasar Sin daya ne daga cikin nasarorin gwamantin jihar na janyo masu saka jari 'yan kasashen waje.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kwamanshinan masana'antun na jihar Kano ya ci gaba da cewa a yanzu haka akwai alamomin masu yawan gaske dake nuna matsayin jihar Kano zai sake dawowa na jiha mafi yawan hada-hadar kasuwanci a Najeriya, saboda damarmaki da dama da gwamnatin jihar ta bullo da su ga dukkan masu sha'awar zuba jari a jihar.

Ya ce a shirye gwamnati take ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga 'yan kasuwa na cikin gida da na kasashen waje.

Ya shaidawa 'yan kasuwar ta kasar Sin cewa jihar Kano jiha ce mai zaman lafiya tare kuma da dinbun albarkatun kasa wadanda ake matukar bukata a kasuwannin duniya.

A jawabin sa jagoran ayarin 'yan kasuwar Mr. Diao Shengyun ya ce sun zo jihar Kano ne domin duba hanyoyin saka jari a bangarorin masana`antun sarrafa shinkafa da na samar da takin zamani kana da na samar da injinan aikin gona na zamani.

Kuma sun yanke shawarar zuwa Kano saboda kyakkyawan yanayin da gwamantin jihar ta samar ga masu saka jari 'yan kasashen waje.

Ya ce a cikin tawagar tasu akwai shugabannin kamfanoni da kuma 'yan kasuwa wadanda dukkannin su sun gamsu da saka jarin su a wadannan bangarori guda uku domin cin moriyar kowanne bangare.

Mr. Shengyun ya ce tuni suka yanke shawarar assasa kamfanin sarrafa shinkafa na buliyoyin naira a jihar ta Kano, domin tallafawa kokarin gwamantin jihar ta Kano wajen samar da wadataccen abinci.(Garba Abdullahi Bagwai)