logo

HAUSA

An kammala bikin Canton Fair cikin nasara a yau

2024-05-05 20:48:39 CMG

Yau Lahadi 5 ga wata, aka kammala bikin baje-kolin hajojin da ake shigowa gami da fitar da su zuwa ketare na kasar Sin, wanda aka fi sani da suna Canton Fair karo na 135 cikin nasara. Yawan baki ‘yan kasuwan kasashen waje da suka halarci bikin ya kai wani sabon matsayi a tarihi.

Ya zuwa ranar 4 ga watan Mayu, masu sayayya 246,000 da suka fito daga kasashe da yankuna 215 sun halarci bikin a zahiri, wanda ya karu da 24.5% idan aka kwatanta da wanda ya gabata. Daga cikin su, akwai masu sayayya 160,000 daga kasashen da ke cikin hadin gwiwar raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", adadin da ya karu da 25.1%.

Kaza lika, ya zuwa ranar 4 ga watan Mayu, yawan cinikayyar da aka yi a zahiri da ta shafi fitar da kayayyaki zuwa ketare a baje kolin Canton Fair na bana, ya kai dalar Amurka biliyan 24.7, wanda ya karu da kashi 10.7% idan aka kwatanta da wanda da ya gabata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)