logo

HAUSA

Jimilar kamfanonin samar da kayayyaki masu sayar da hannun jari a kasar Sin ya kai 3,629 zuwa karshen watan Maris na bana

2024-05-05 16:23:14 CMG Hausa

Zuwa karshen watan Maris na bana, kasar Sin na da jimilar kamfanonin samar da kayayyaki 3,629 dake sayar da hannayen jari a kasuwar hannayen jari ta cikin gida.

Galibin kamfanonin dake kasar Sin na mayar da hankali ne ga bangarorin da suka shafi samar da kayayyaki, da watsa bayanai, da tsara manhajoji, da hidimomin fasahar sadarwa, da sari da sayar da kayayyaki.

Zuwa karshen watan Maris na bana, kamfanonin da aka yi rejistar sunayensu a kasuwar hannyen jari ta birnin Shanghai sun kai 2,272, da 2,851, a kasuwar hannayen jeri ta Shenzhen, sai da kuma wasu 247, da aka yi wa rajista a kasuwar dake birnin Beijing na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)