logo

HAUSA

Bincike: Kamfanonin kasashen waje na da karin kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Sin

2024-05-04 15:48:46 CMG Hausa

Wani bincike kan kamfanoni sama da 600 na kasashen waje da hukumar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta gudanar, ya nuna cewa, wadannan kamfanoni na kara kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Sin.

Fiye da kashi 70 cikin 100 na kamfanonin da aka gudanar da binciken a kansu suna da kyakkyawar fata game da kara bunkasuwar kasuwar kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa, wanda ya karu da kusan maki kashi 3.8 cikin 100 idan aka kwatanta da rubu’in da ya gabata.

Fiye da rabin kamfanonin da aka yi binciken a kansu sun yi imanin cewa, kasuwar kasar Sin ta samu karin armashi, wanda ya karu da maki kashi 2.9 cikin 100 bisa adadin da aka samu a rubu’in da ya gabata.

Bugu da kari, fiye da rabin kamfanonin suna tsammanin zuba jari a kasar Sin zai samar da karin riba a cikin shekaru biyar masu zuwa. A cikin wadannan kamfanoni, kashi 60 cikin 100 sun fito ne daga Turai. (Yahaya)