logo

HAUSA

Rundunar sojojin Amurka: An kashe farar hula a kasar Syria

2024-05-04 16:02:58 CMG Hausa

Cibiyar kwamanda ta tsakiya ta kasar Amurka ta sanar a kwanan baya cewa, sojojin kasar sun kashe wani farar hula a wani harin da aka kai kasar Syria daga sama a shekarar bara.

A cikin wata sanarwar da cibiyar ta gabatar, an ce a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2023, sojojin kasar Amurka sun yi amfani da wani jirgin sama maras matuki wajen kashe wani mutum dan kasar Syria mai suna Lufti Hassan Masto. Inda a lokacin, a cewar sojojin kasar Amurka, aka yi tsammanin cewa, shi wani madugun kungiyar ta'addanci ta al-Qaeda ne. An bayyana a cikin sanarwar cewa, an kai wannan hari ne bisa umarnin ma'aikatar tsaron kasar Amurka, da na cibiyar kwamanda ta tsakiya ta kasar. Sai dai an ce ba za a iya samar da karin bayani ba, sakamakon yadda aikin binciken lamarin ya shafi bayanan sirri.

Yayin da gidan telabijin na Al Jazeera ke watsa labarin, ya yi sharhi da cewa, ko da yake mutanen duniya sun riga sun shaida dimbin hare-haren da sojojin kasar Amurka suka kai kan fararen hula na kasashe daban daban, amma kusan ba a taba dorawa wani jami'in kasar Amurka laifi, da yanke masa hukunci ba, kana da wuya ne iyalan wadanda suka rasu su samu diyya daga bangaren Amurka.(Bello Wang)