logo

HAUSA

Shugaban Serbia: Kullum shugaba Xi Jinping ya cika alkawarinsa

2024-05-04 16:10:25 CMG Hausa

Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya yi hira da ‘yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a kwanan nan. Yayin da aka ambaci ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Serbia, Vucic ya ce, yana fatan ganawa da shugaba Xi Jinping, ziyarar nan zai kawo damammaki masu kyau ga al’ummar Serbia.

Vucic ya bayanna cewa, a ganinsa, shugaba Xi Jinping yana da kirki, zai cika dukkanin alkawuransa. Kasar Serbia tana farin ciki sosai wajen shiga aikin gina shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya tare.

Kazalika, jimillar cikinikkayar dake tsakanin kasashen Serbia da Sin ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 6.1, kuma yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ‘yanci da kasashen biyu suka sa hannu za ta sanya jimillar cinikayyar bangarorin biyu ta ninka sau 2 ko sau 3 bisa yadda take a halin yanzu a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Vucic ya kara da cewa, shugaba Xi shugaba ne da ya ba da gudummawa wajen daina yaki da kafa zaman lafiya na dogon lokaci. Ya yi kira ga saura da su ji shawarwarin shugaba Xi, su yi sasantawa don cimma matsaya daya, saboda a karshe dai abin da ya shafi bil'adama shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Safiyah Ma)