logo

HAUSA

Majalissar wakilan Najeriya ta ce za ta hada kai da sabuwar hukumar lura da rayuwar almajiran ta kasar

2024-05-04 15:41:05 CMG Hausa

Majalissar wakilan Najeriya ta ce a shirye take ta yi aiki tare da hukumar lura da harkokin almajirai da makarantun tsangaya na kasar wajen tabbatar da ganin yara sama da miliyan goma dake kasar sun koma makaranta.

Shugaban kwamatin ilimin musamman na majalissar Hon Al`Mustafa Aliyu ne ya tabbatar da hakan lokacin da shugaban hukumar ya ziyarce shi a majalissar,ya ce babu shakka wadata yara da ilimin zamani da na addini zai sanya Najeriya cikin kasashe da suke da kyakkyawar makoma ta fuskar tattalin arziki da zaman lafiya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Hon Almustafa ya ce yana daya daga cikin burin majalissar dokoki ta kasa kyautata sha`anin koyo da koyarwa a dukkan matakai, wannan ce ta sanya ma majalissar bata wasa da duk wasu kudirori da suke da nasaba da cigaban ilimi a kasa baki daya.

Shugaban kwamatin ilimin musamman na majalissar dokokin ta tarayyar Najeriya ya yi fatan cewa sabuwar hukumar za ta fitar da gwamnati da al`ummar kasa kunya ta hanyar kawo sabbin tsare tsare a fagen sha`anin almajirci da kuma harkokin makarantun tsangaya dake arewacin kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai dake zauren majalissar, shugaban hukumar Alhaji Idris Muhammad Sani ya ce ya ziyarci majalissar ne domin neman hadin kai game da yadda za su tunkari kalubalen dake gaba na mayar da miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta cikin aji.

“ Na farko dai abun da muke so cikin wata biyun nan, mu tabbatar da iyaye da malamai da shugabannin al`umma da sarakuna sun fahimci makasudin kudirin shugaban kasa a kan wannan al`amari daya shafi almajirci ,sannan kuma muna so mu samu tabbatattun alkaluma na wadannan yara domin samun wadannan alkaluma zai ba mu damar yin tsare-tsare mai kyau, haka kuma zai ba mu damar gamsar da mutane daga kasashen waje cewa su zo su shiga cikin harkan nan a yanzu ba kamar a baya ba”.(Garba Abdullahi Bagwai)