logo

HAUSA

An gabatar da rahoto dangane da hadin gwiwar da kasar Sin da kasashen Turai suke yi a fannin kare muhalli

2024-05-04 16:07:12 CMG Hausa

A jiya Juma'a, an gabatar da rahoton bincike dangane da hadin gwiwar da kasar Sin da kasashen Turai suke yi, a fannin kare muhalli da tinkarar sauyin yanayi.

Bangarorin da suka wallafa rahoton sun hada da cibiyar nazarin tunanin kare muhallin halittu na Xi Jinping ta kasar Sin, da cibiyar aikin tsimin makamashi ta kasar, da dai sauransu. Kana a cikin rahoton binciken, an bayyana cewa, kamata ya yi kasar Sin, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, da kungiyar kasashen Turai, wadda ta kasance hadaddiyar kungiyar kasashe masu sukuni mafi girma a duniya, su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu, inda za su rika hadin gwiwa da juna a fannonin kare muhallin halittu, da tinkarar sauyawar yanayi, don neman tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya da na al'ummar dan Adam, cikin wani yanayi mai dorewa.

An kara bayyana a cikin rahoton cewa, bangarorin Sin da Turai suna da tunani iri daya na neman samun ci gaban tattalin arziki gami da kokarin kare muhalli, wanda ya zama tushen hadin gwiwarsu. Kana yin hadin kai a tsakanin bangarorin 2 ba ma kawai ya dace da moriyar junansu ba, har ma zai amfanar da daukacin duniya, ganin yadda hadin gwiwarsu zai samar da karin damammaki na tinkarar sauyawar yanayi na duniya, da farfado da tattalin arzikin kasashe daban daban. (Bello Wang)