logo

HAUSA

Sojojin Amurka da sojojin Rasha masu ba da horo na makwabtaka da juna a wani sansanin soja da ke Yamai

2024-05-04 21:34:33 CMG Hausa

Sojojin Rasha sun dauki hedkwatarsu a wani sansanin soja da ke Yamai, inda kuma sojojin Amurka suke zaune, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya rawaito kalaman wani jami’in Amurka. Alhali kuma sojojin da suka karbi mulki a Nijar sun bukaci ficewar sojojin Amurka daga kasar baki daya.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan batu ga kuma rahoton da ya hada mana.

Da ake tambayarsa kan wannan batu, sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin bai dauki abin da gautsi ba a ranar jiya Jumma’a 3 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da kawar da duk wani hadari ga sojojin Amurka ko yiwuwar sojojin Rasha su kusanto kayayyakin soja na Amurka.

Mulkin soja a Nijar da ya biyo bayan wani juyin mulki na ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, ya yi allawadai a cikin watan Maris da yarjejeniyar soja da ke aiki tare da Amurka, ganin cewa kasancewar sojojin Amurka, da ke cikin tsarin yaki da ta’addanci, ba ta bisa ka’ida.

Hukumomin Washington sun amince a tsakiyar watan Afrilu na janye sojojinsu.

Sojojin Nijar sun sanar da hukumar Joe Biden da kasancewar sojojin Rasha a birnin Yamai su kusan 60, adadin da rundunar sojojin Amurka ba ta tabbatar da shi ba, in ji jami’in Amurka.

Bayan juyin mulkin da ya kifar da Mohamed Bazoum, nan da nan sabbin shugabannin Nijar suka yi waje da sojojin Faransa daga kasar tare da kusanto kasar Rasha, kamar Mali da Burkina Faso.

A cewar wani jami’in Pentagone, da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa sojojin Rasha ba su jira tafiyar sojojin Amurka suka kama hedkwatarsu a wata rumfa da ke sansanin soja mai lamba 101 da ke filin jirgin kasa da kasa na Diori Hamani da ke birnin Yamai, inda sojojin Amurka suke ciki.

Kasar Amurka na da sojoji dubu guda a Nijar, da ke tsakanin birnin Yamai da birnin Agadez da ke arewacin kasar, inda suke aikin sanya ido da yaki da ta’addanci har zuwa kasar Libiya. A Nijar, Amurka na da wani sansanin jiragen yaki masu sarrafa kansu mafi girma kusa da birnin Agadez, da aka kashe miliyan 100 na dalar Amurka wajen ginawa.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.