Hedikwatar tsaron Najeriya tace ta kammala bincike a game harin bama-bamai da aka kai kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna
2024-05-03 15:36:40 CMG Hausa
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce sojojin da aka kama da laifi a harin bomb da aka kai kauyen Tudun Biri dake jihar Kaduna zasu gurfana gaban kotun soji domin fuskantar hukunci.
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Major Janaral Edward Buba ne ya tabbatar da hakan ranar alhamis 2 ga wata a birnin Abuja.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Idan dai za a iya tunawa a ranar 3 ga watan disambar bara ne wani harin jirgi mara matuki mallakin rundunar sojin Najeriya ya kai harin ga wasu al`umomin a kauyen Tudun biri dake yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna wanda yayi sanadin mutawar a kalla fararen hula 85.
“An kammala bincike a kan hadarin da ya faru a kauyen Tudun biri, tun farko ma dai bai kamata a ce abun ya faru ba, kuma duk wadanda suke da hannu za su fuskanci shari` a a kotun soji a game da abun da suka aikata”
Haka kuma major janaral Edward Buba ya sanar da cewa dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutane 465 da masu garkuwa da mutane suka sace, yayin da kuma aka kashe yan ta`adda 715 cika har da daya daga cikin manyan kwamandojojin su a jerin farmaki daban daban da aka kai maboyar su.
“An samu halaka wasu daga cikin `yan ta`adda ne a yankin Kwalaram dake yankin tafkin Chadi, haka kuma an tarwatsa sansanin `yan tadda dake karkashin Babaru a yankin karamar hukumar kankara a jihar Katsina, sauran sun hada da sansanin `yan ta`adda dake karkashin Bello Turji dake dajin Shinkafi a jihar Zamfara”
Daraktan harkokin yada labaran na hedikwatar tsaron ta Najeriya yace a yayin wannan farmaki dakarun tsaron sun samu kwato muggan makamai da dama a dukkan sansanonin da suka tarwatsa.(Garba Abdullahi Bagwai)