logo

HAUSA

Sin ta harba na’urar Chang’e-6 domin kwaso samfura daga bangaren duniyar wata mafi nisa

2024-05-03 19:42:36 CMG Hausa

A yau Juma’a ne kasar Sin ta harba na’urar binciken duniyar wata Chang’e-6 domin tattara da kuma dawo da samfura daga bangaren duniyar wata mafi nisa mai ban al’ajabi, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin binciken duniyar wata.

Wata rokar Long March-5, dauke da na’urar Chang’e-6, ta tashi ne daga wurin harba kumbuna na Wenchang dake gabar tsibirin Hainan na kudancin kasar Sin da karfe 5 da mintuna 27 na yamma, agogon Beijing.

Harba na’urar Chang'e-6 ya samu cikakkiyar nasara, a cewar hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin wato CNSA. (Yahaya)