logo

HAUSA

Ministan wajen Hungary na fatan ziyarar Xi za ta bude sabon babi na dangantakar Hungary da Sin

2024-05-03 16:49:27 CMG Hausa

Kwanan nan, ‘yar jarida ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta yi hira da ministan harkokin wajen kasar Hungary Szijjártó Péter, wanda ya kawo ziyara a Sin.

Yayin zantawar, Szijjártó ya bayyana cewa, Hungary ta dade tana dora muhimmanci ga dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da Sin, tana fatan ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasarsa za ta bude sabon babi na dangantakar kasashen biyu.

Szijjártó ya ce, bangaren Hungary ya yi farin ciki ga ziyarar aiki da shugaba Xi zai kai a kasar. Bana ta cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Hungary da Sin, Hungary ta dade tana dora muhimmanci kan dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da jamhuriyyar jama’ar kasar Sin. Bangaren Hungary na fatan ziyarar aiki da shugaba Xi zai kai a kasar zai bude sabon babi na dangantakar tsakanin kasashen biyu. A karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kasashen biyu suna shirin yin hadin gwiwa wajen gina manyan ababen more rayuwa. Ban da hakan, bangaren Hungary na fatan kasashen biyu su ci gaba da gudanar da hadin gwiwar sabon nau’in hada-hadar kudi tsakaninsu.

Szijjártó ya kara da cewa, bangaren Hungary ya yi imanin cewa, ziyarar aiki da shugaba Xi zai kai a Hungary zai kara ingancin dangantakar bangarorin biyu. Kuma yana fatan gudanar da wasu ayyukan bunkasa masana’antu karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da Sin ta gabatar. (Safiyah Ma)