logo

HAUSA

Fitowar rana mai ban mamaki a ranar jiya da safe a sararin samaniyar birnin N’Konni

2024-05-03 15:43:00 CMG Hausa

Mu je a jamhuriyyar Nijar, musammun ma a birnin N’Konni da ke yankin Tahoua inda mazauna birnin suka wayi gari da fitowar rana ta zo da abin mamaki a ranar jiya Alhamis 2 ga watan Mayun shekarar 2024, lamarin da ya janyo ayar tambayoyi daga mutanen nan na birnin N’Konni

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Al’umomin birnin N’Konni da ke cikin yankin Tahoua, sun wayi garin ranar jiya Alhamis 2 ga watan Mayun shekarar 2024 da sanyin safiya da wata fitowar rana mai cike da mamaki da ban al’ajabi. Hakika, nan da nan da fitowar rana daga kowane bangarenta na hannun dama dana hagum, da wasu kananan da’irori masu haske da suka sanya rana a tsakiya, tamkar wasu kananan rana guda biyu.

Cikin mamaki da al’ajabi, mutane suka fara cewa yau dai rana ta fito tare da diyanta biyu ganin abu ne da ba a saba ganin irinsa ba a tarihin birnin N’Konni da ke cikin yankin Tahoua.

Abu kuma na biyu, wanda ya bada mamaki da ban al’ajabi nada nasaba fitowar rana da kaloli kamar wani bakan gizo a sararin samaniya, lamarin da ya janyo ayar tambayoyi bisa ga wannan al’amari.

Saidai kwararru a fannin ilimin yanayi, hasashen yanayi, da ruwa da kuma tarihi sun yi mamakin irin wannan al’amari da ya faru a sararin samaniyar birnin N’Konni.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriiyar Nijar.