Wakilin Sin ya jaddada muhimmancin neman ci gaba na bai daya
2024-05-03 15:50:34 CMG Hausa
Mataimakin zaunannen walilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, a jiya Alhamis ya yi jawabi a muhawarar yau da kullum ta babban taron Majalisar dangane da batun zaman lafiya da al'adu, inda ya jaddada muhimmancin zama daidai wa daida tsakanin mabambantan kasashe, da amincewa da junansu, da tabbatar da ci gabansu na bai daya, gami da yin koyi da juna a tsakanin al'adun kasashe daban daban.
A cewar jami'in kasar Sin, a halin da ake ciki yanzu, duniyarmu na fama da matsaloli a fannonin kiyaye zaman lafiya, da neman ci gaban tattalin arziki, da tsaro, gami da gudanar da mulki. Kana a dimbin wurare daban daban ana ta fama da matsalar rashin daidaituwa, da ta rashin kulawa da sauran bangarori masu ruwa da tsaki. Wannan yanayi, a cewar jami'in, ya nuna wajibcin inganta al'adu mai daukaka zaman lafiya.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, da farko, ya kamata a yi kokarin tabbatar da daidaituwa da amincewa da juna tsakanin mabambantan al'ummu, saboda su ne tushen tsaron duniya.
Sauran shawarwarin da ya gabatar sun hada da, na biyu, kokarin neman samun ci gaban tattalin arziki na bai daya a duniya. Da na uku, kokarin koyi da juna a tsakanin wayewar kai da al'adu daban daban. Kasar Sin na son kokarin aiki tare da sauran kasashe daban daban, don tinkarar kalubalolin da duniyarmu ke fuskanta, da gina al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya bisa hadin gwiwarsu, in ji jami’in na kasar Sin. (Bello Wang)