logo

HAUSA

An fara sayar da littafin "Xi Jinping da abokansa daliban jami'a" a kasuwannin Sin

2024-05-03 15:48:50 CMG Hausa

Madaba'ar matasa ta kasar Sin ta samar da littafin bugu na 2 na jerin littattafai mai taken "Xi Jinping da abokansa daliban jami'a" a kwanan baya, ta yadda aka fara sayar da littafin a kasuwannin kasar Sin.

An taba gabatar da littafin bugu na farko na jerin littattafan a watan Nuwamban shekarar 2020, wanda ya samu karbuwa sosai tsakanin daliban jami'o'i daban daban na kasar Sin. Kana a cikin wannan bugu na biyu, an ci gaba da yin amfani da tsarin wallafa bugu na farko, inda aka bayyana labaru dangane da yadda shugaba Xi Jinping ya yi rangadi a jami'o'in kasar Sin, gami da kulawa da dalibai, da kuma ba da jagoranci kan harkokinsu, ta wasu bayanan hirarraki guda 24.

Ta wadannan labaru da bayanai, an nuna yadda shugaban na kasar Sin ke dora muhimmanci kan ci gaban harkokin dalibai matasa, da yadda ya zama abin koyi a kokarin zama mai fahimtar matasa, da mai kulawa da su, kuma wanda ke musu jagora dangane da harkokinsu na raya kai. (Bello Wang)