logo

HAUSA

Matashin dan tseren mota na kasar Sin ya bayyana fatan karin matasa Sinawa za su shiga a dama da su a wasan

2024-05-02 20:50:04 CMG Hausa

Zhou Guanyu, matashin dan wasan tseren motoci ne ajin kwararru ko “Formula One”, wanda a bana ya shiga aka fafata da shi a babbar gasar kasa da kasa ta tseren motoci da ta gudana a birin Shanghai, gasar da aka yiwa lakabi da “Chinese Grand Prix”. Wannan ne dai karon farko da Zhou ya halarci babbar gasar “Formula One Shanghai” ko F1 Shanghai” a gida. Yayin da ya fitar da motarsa domin tseren wanda aka bude a babban filin tseren motoci na Shanghai International Circuit, Zhou Guanyu ya kasa boye farin ciki da alfaharinsa.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Zhou ya ce "Ni yaro ne daga Shanghai, wanda ke sha’awar nunawa duniya sauyin da ake samu a kasar Sin game da wasan tseren motoci, tare da share fagen baiwa karin matasa masu basirar wannan wasa damar haskawa a dandalin kasa da kasa". Zhou ya ce yana fatan karin matasa Sinawa za su shiga a dama da su a wannan fage, wanda hakan zai zaburar da sashen masana’antar wasan tseren motoci a kasar.

Game da muhimmancin gasar ta “F1 Shanghai”, Zhou ya ce "Ba don wannan gasa ba, da ban samu mafari na shiga wannan wasa ba, kana da ban tsaya a nan a matsayin direba shekaru 20 bayan na zo nan a matsayin dan kallo ba. A wannan karo, gani na zo gida domin a fafata tare da ni. A gani na gasar F1 ta “Chinese Grand Prix”, ta bude kofofi ga direbobin motocin tsere na kasar Sin, na shiga a dama da su a gasannin kasa da kasa".

A shekarar 2004, Sin ta karbi bakuncin gasar a karon farko. A wancan lokacin, Zhou ya zauna kan kujera mai lamba 24, domin kallon tseren motoci a gasar ta “Chinese Grand Prix”, an kuma yi dace a wannan lokaci, Zhou ya yi tsere da mota mai lamba 24.

Da yake tsokaci game da ci gaban da ya samu, daga dan kallo zuwa matukin motar tsere, Zhou ya ce da zai yiwu da ya baiwa kansa lokacin yana karami shawarar dagewa wajen cimma mafarkinsa, da rungumar takara ba tare da wani tsoro ba.

Ya ce "A shekarar 2004, ina yaro wanda ke zaune a kujera mai lamba 24, ina kallon tseren motoci a nan, lokacin ban san komai game da tseren motoci ba. Daga baya, na ci gaba da shiga wasanni daban daban. Da zan iya, da na gayawa kai na lokacin ina karami da cewa, “ci gaba da kwazon cimma burin ka, kana kokari kwarai da gaske. Kar ka ji tsoron gasa ko takara, ka yarda da kan ka, sauran ‘yan wasan tseren motoci na waje ba su fi ka da komai ba".

Game da kalubalen da ‘yan tseren motoci na Sin ke fuskanta yayin da suke shiga wasannin da ake yi a turai, Zhou ya amince cewa "A wurin da ba a saba da shi ba, inda ba mai nunawa mutum hanyar gudanar da wasa, mutum shi kadai ne sai ‘yan tawagarsa, tun daga shiga wasan a matsayin nishadi zuwa kaiwa matsayin kwarewa lallai akwai kalubale. Mutum na iya zama gwani a kasarsa, amma a turai, yana iya ganin sa’anninsa, abokan fafatawa a filin tsere sun fi shi kwarewa nesa ba kusa ba. Ya ce “Kaiwa ga shiga gasar F1, tafiya ce mai cike da shingaye da matsaloli, amma duk da haka ban taba nadamar ta ba".

Tun bayan fara wasa a gasar F1 a shekarar 2022, Zhou ya lashe kofuna da dama, inda a shekarar ta 2022 ya lashe lambar “Best Rookie”, tare da kasancewa dan wasa mai hazaka na 8, a gasar da ta gudana a Canada, ya kuma yi nasarar samun gurbin shiga babbar gasar Hungary ta 2023 a matsayi na 5.

A cewarsa "Duk wani matsayi da na cimma yana da muhimmanci. Duk wata nasara da na samu tana ci gaba da zaburar da ni wajen kara yunkurawa gaba. A wannan gaba, gasar F1 ta shekarar 2024 ta kasar Sin, ta kafa tarihin cika shekaru 20 da fara gudanar da tseren motoci na Shanghai. A nawa bangare tun bayan fara shiga ta gasar F1, ina ta fatan zuwa gasar birnin Shanghai. Wuri ne da zan iya cewa na saba, kuma ban saba da shi ba, domin gina ne gare ni, amma wannan ne karon farko da nake fafatawa a gasar ta nan. Ina samun karin karfin gwiwa saboda buri na da na ‘yan kallo na na cimma nasara. Ina fatan zan fi taka rawar gani a gida, na jima ina yin horo kan na’urar kara kwarewa ta wannan fili. Duk da ban taba yin wasa a nan ba, ina ga na shiryawa wurin sosai".

Domin nuna kaunarsa da gida, Zhou ya shiga gasar ta birnin Shanghai da hular kwano mai dauke da zanen sanannun wurare dake birnin, ciki har da taswirar layin dogo ta Shanghai, da wurare daban daban masu ban sha’awa dake birnin, ciki har da lambun Yuyuan, da gadar Waibaidu, da yankin hada hadar kudade na Lujiazui.

Zhou ya ce "Wadannan ne abubuwa da nake fatan nunawa duniya. Cewa ni direba ne daga Shanghai. Ina fatan nunawa duniya ci gaban fannin tseren motoci na Sin, tare da fatan karin matasa Sinawa dake wannan wasa za su kai ga taka rawa a dandamalin kasa da kasa. Idan na tsufa kuwa, na kai ga kammala wasa, ina fatan zan taimakawa karin matasa direbobi, da hanyoyin cimma burin su na wasan tseren motoci, ta hanyar raba kwarewa ta da na samu a tsawon shekaru, kana in nuna musu hanyar cimma nasara".

Zhou na fatan a nan gaba, zai karfafa gwiwar zuri’o’i masu yawa, hanyar kaiwa ga zama zakaru a kakar wasanni dake tafe.

Game da wannan batu, jagoran gasar F1 mista Stefano Domenicali, ya yi karin haske kan muhimmancin sake dawowa kasar Sin da babbar gasar, tare da lalubo hanyoyin kara gina wasan tseren motoci a kasar, bayan dawowa Shanghai a karon farko tun bayan shekarar 2019.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gabar da ake bikin cikar “Chinese Grand Prix” shekaru 20 da kaddamarwa, mista Domenicali ya ce "A bangaren mu muna kara mayar da hankali zuwa nan, kuma tabbas muna fatan tabbatar da harkokin wasannin mu a wannan yanki".

Duk da cewa ya gama gasar ta wannan karo ta birnin shanghai a matsayi na 14, direban motar tsere ta kamfanin Sauber, matashi Zhou Guanyu, ya ci gaba da kasancewa mai matukar jan hankalin ‘yan kallo a filin wasan da gasar ta gudana.

Mazauna birnin Shanghai sun rika bibiyar duk wani motsa da Zhou ya yi tare da Shewa, da nuna masa goyon baya a matsayinsa na wakilin birnin, musamman ma daga bangaren wadanda suka kalli gasar ta “Chinese Grand Prix” a karon farko. A nasa bangare kuwa, Zhou ya cika da shauki lokacin da ya fito daga motarsa kirar kamfanin Sauber a karshen tseren da ya kammala.

A ganin mista Domenicali, matashi Zhou na da kwarewa, da karsashin cimma karin nasarori, da ma tasirin da ka iya bunkasa gasar F1 a kasar Sin.