logo

HAUSA

Sin ta ba da rahoton tafiye-tafiye da jiragen kasa a ranar 1 ga watan Mayu

2024-05-02 20:04:06 CMG Hausa

Tafiye-tafiyen da fasinjoji suka yi da jiragen kasa a kasar Sin ya kai sama da miliyan 20.69 a ranar Laraba, ranar farko na hutun kwanaki biyar na hutun ranar ‘yan kwadagon kasa da kasa, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi, kamar yadda bayanai daga kamfanin layin dogo na kasar ya nuna.

Kamfanin layin dogo na kasar Sin ya ce ana sa ran yin tafiye-tafiyen fasinjoji miliyan 17 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,094 da aka shirya. (Yahaya)