logo

HAUSA

Kungiyar kwadago a tarayyar Najeriya ta baiwa hukumar lura da harkokin wutan lantaki kasar wa 'adin dakatar da karin farashin wuta

2024-05-02 15:40:20 CMG Hausa

Kungiyar Kodago a tarayyar Najeriya ta baiwa hukumar lura da harkokin wutan lantarki na kasar wa`adin mako guda data dakatar da Karin farashin wuta data yi kwanan nan.

A lokacin da yake jawabi yayin bikin ranar ma`aikata jiya talata 1 ga watan Mayu a filin wasa na Eagle square dake birnin Abuja, shugaban kungiyar Kodago na kasa Mr Joe Ajaero ya bayyana rashin gamsuwa bisa yadda ake cigaba da samun matsalar karancin wuta a kasar baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban kungiyar kwadagon a tarayyar Najeriya ya ce karancin wutar da ake fuskanta yana mutukar shafar bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Akan batun karin albashi kuwa, shugaban kungiyar kwadagon ya ce har yanzu kungiyar na nan kan matsayin ta neman karin albashin da zai iya dauka dawainiyar ma`aikaci da iyalin sa dai dai gwargwado.

“Sakon mu a bayyana ne suke, duk albashin daya gaza iya tallafawa rayuwa, tabbas zai iya kai ga ma`aikaci cikin halin talauci”

A jawabin sa yayin bikin, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yabawa yayi bisa irin gudumowar da ma`aikata ke bayarwa wajen gina kasa.

Sanata Kashim Shettima ya ce kamar yadda kowa ya sani ne tattalin arzikin Najeriya ya tsinci kansa cikin wani hali,a sakamakon haka ne gwamanti take gudanar da ayyukanta daidai da karfin aljihun ta.

“Idan dai za ku iya tunawa a cikin watan janairun 2024 gwamnatin tarayayr ta kafa kwamati mai mutane 37 a kan batun sabon tsarin mafi kankantar albashi, kuma an dorawa kwamatin alhakin gabatarwa majalissar zartarwa ta kasa tsarin albashin da zai dace da yanayin tattalin arzikin na yanzu, kuma tun daga wannan lokaci kwamatin yake aiki tare da kungiyar kodago domin fitar da sabon tsarin albashin”

Kamar dai yadda mataimakin shugaban kasar ya fada kawo yau kwamatin bai kammala zartar da shawara ba, amma akwai tabbacin cewa sabon tsarin albashin zai fara ne daga wannan wata na Mayu.(Garba Abdullahi Bagwai)