Shugban kasar Serbia ya aza harsashin aikin gina wani babban filin wasan kwallon kafa da wani kamfanin Sin zai gudanar da shi
2024-05-02 15:12:23 CMG Hausa
A jiya Laraba, bisa agogon kasar Serbia, an yi bikin aza harsashin aikin gina babban filin wasan kwallon kafa na kasar, da wani kamfanin kasar Sin zai dauki nauyin gudanar da shi, a Belgrade, fadar gwamnatin kasar Serbia.
Wannan sabon filin wasan kwallon kafa, gami da gine-ginen cibiyar baje kolin kayayyakin kasashe daban daban ta EXPO, za a gina su ne a kudu maso yammacin birnin Belgrade. Bayan an kammala aikin ginin, sabon filin wasan kwallon kafan zai iya daukar masu kallo kimanin dubu 52, yayin da cibiyar baje kolin kayayyakin za ta zama daya daga cikin manyan dakunan baje kolin kayayyakin cinikayya mafi girma a kudu maso gabashin nahiyar Turai. Kana a hade suke, wadannan gine-gine za su zama wadanda ke wakiltar birnin Belgrade.
Shugaban kasar Sebia, Aleksandar Vucic, ya halarci bikin aza harsashin, inda kuma ya yi jawabin cewa, yana sa ran ganin a aiwatar da ayyukan ginin yadda ake bukata. Ya ce yana godiya ga kasar Sin, kan yadda ta samar da dimbin taimako ga kasar Serbia, don ta samu damar raya kanta. Ban da haka, ya ce yana fatan ganin jama'ar kasarsa za su yi kokari tare da abokansu na kasar Sin, don kammala aikin ginin mai matukar muhimmanci bisa shirin da aka tsara.
A nashi bangare, Li Ming, jakadan kasar Sin dake kasar Serbia, ya gode ma shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic da gwamnatinsa, kan yadda suke da cikakken kwarin gwiwa kan kamfanonin Sin, da yadda suke goyon bayan baiwa wani kamfanin kasar Sin damammaki na gina babban filin wasan kwallon kafa mai matsayin kasa, da cibiyar baje kolin kayayyakin kasa da kasa ta EXPO, duk a kasar ta Serbia. (Bello Wang)