logo

HAUSA

Ma'aikatan Nijar tare da na kasashen duniya baki daya sun yi bikin ranar 1 ga watan Mayu ko sallar ma'aikata

2024-05-02 15:47:29 CMG Hausa

Bikin sallar ma'aikata ta duniya a Nijar ta gudana a wannan shekara cikin wani yanayi na musammun, tare da daukar wata sabuwar alkibla cikin tarihin Nijar, bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, inda ma’aikata sun dandana wahalhalu sakamakon takunkumin da aka sanya wa kasar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A cikin jawabin da ta gabatar ta gidan rediyo da talabijin na kasa, a jajibirin ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2024, ministar kwadagon Nijar, Madam Aissatou Abdoulaye Tondi ta jinjinawa ma'aikatan Nijar kan juriyarsu da kuma fuskantar matsala ba tare da kasala ba. Haka kuma ta nun yabo da girmamawa ga dukkan kungiyoyin kwadago na kasa, da suka nuna goyon bayansu a kai a kai ga kwamitin ceton kasa na CNSP, domin wata kasar Nijar mai cike da ci gaba da daukaka da kuma 'yanci.

A cewar ministar kwadago, a tsawon lokacin da ya gabata, kasar Nijar ta tsara ayyuka da dama da ke da manufar kyautata mulki na gari a fannin kwadago da kuma kare ma'aikata. Kamar yadda aikinta ya tanada, Madam Aissatou Abdoulaye Tondi, ba tare da wani kewaye ba ta tabo daga cikin abubuwan da suka shafi ma’aikatarta batun kawo gyaren fuska kan matsayin ma'aikacin gwamnati domin shaye hawayensu kan wasu koke kokensu, da ke cikin bukatun ma'aikata, da kuma yarjejeniyar da aka sanyawa hannu tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago, da kuma ci gaba da ayyukan dindindin da ke shafar kyautatuwar yanayin aiki da na rayuwar ma'aikata, da suka hada da ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu a Nijar. Inji ministar ma’aikatan Nijar a cikin jawabinta.

Duk dai a ranar ta jiya 1 ga watan Mayun shekarar 2024, kawancin kungiyoyin kwadago biyar da suka hada da USTN, CNT, CDTN, CGSL-NIGER da USPT sun gudanar da fareti tare da mambobin kungiyoyinsu a wurare daban daban na birnin Yamai da kuma cikin jahohin kasa, inda a yayin wadannan bukukuwa da fareti, ma’aikatan Nijar a karkashin wadannan kawancen kungiyoyin kwadago guda biyar sun mikawa ministar kwadago koke kokensu, wacce kuma ta bayyana niyyar gwamnatin rikon kwarya a karkashin jagorancin faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine da kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kuma shugaban kasa Abdourahamane Tiani na yin iyakacin kokarinsu domin tabbatar da makoma mai kyau ga ma’aikatan Nijar baki dayansu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.