logo

HAUSA

Sin na adawa da kalaman Amurka na karfafa kasancewar Taiwan a taron WHO

2024-05-02 20:15:48 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ba ta gamsu ba kuma tana adawa da sanarwar da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bayar, inda ya ce Amurka tana matukar karfafawa hukumar lafiya ta duniya WHO gwiwa da ta gayyaci Taiwan ta halarci taron na WHO na bana. (Yahaya)