Darajar cinikayya tsakanin Sin da kasashe mambobin BRICS ta karu da kaso 11.3 a rubu’in farko na bana
2024-05-01 15:40:37 CMG Hausa
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, darajar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar BRICS, ta kai yuan triliyan 1.49, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 209.7, a cikin rubu’in farko na bana, adadin da ya karu da kaso 11.3 bisa makamancin lokacin bara.
Hukumar ta ce wannan adadi shi ya dauki kaso 14.7 na jimilar cinikayyar Sin da kasashen waje a wannan lokaci.
Daga cikin mambobin na BRICS, kuma a matsayinta na babbar abokiyar ciniyayya ta kasar Sin a nahiyar Afrika tsawon shekaru 14 a jere, Afrika ta Kudu ta samu ci gaba sosai a cinikayyarta da Sin. Kuma cikin rubu’in na farko na bana, jimilar kayayyakin da Sin ta kai Afrika ta Kudu ta kai yuan biliyan 35.11, yayin da kasar ta kawo kasar Sin ya kai yuan biliyan 66.46.
Bugu da kari, kasar Sin tana aiwatar da hadin gwiwa da Masar da Habasha a bangaren kayayyakin more rayuwa, kuma cikin rubu’in na farkon bana, ayyukan kwangila da Sin ta aiwatar a kasashen biyu sun karu matuka. (Fa’iza Mustapha)