logo

HAUSA

Gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana damuwa bisa karuwar sace-sacen jama`a da matsalar rashin zuwan yara makaranta a shiyyar

2024-05-01 15:14:16 CMG Hausa

Gwamnonin jahohin arewacin Najeriya sun bayyana damuwa bisa cigaba da karuwar matsalolin sace-sacen jama a, da rashin shigar yara makaranta rashin tsaro da sauran matsalolin da suke da nasaba da taro a shiyyar.

Yayin taron da suka gudanar jiya talata 30 ga watan Aprilu a garin Kaduna, gwamnonin sunce hakika wadannan jarin matsaloli sune suke dakile cigaban shiyyar cikin hanzari, kuma wajibi ne a shawo kan lamarin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Wannan taro dai shine karo na biyu da gwamnonin suka gudanar cikin shekara guda .

Da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin na arewa kuma gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya yace muddin dai ana bukatar shiyyar arewa ta fita daga cikin wadancan matsaloli sai lallai an kyautata sha`anin tattalin arziki da bullo da matakan gina al`umma.

Yace yanzu arewacin Najeriya shi yafi kowanne bangare a duniya baki daya  yawan yaran da basa zuwa makaranta, wanda kamar yadda yace kalubale ne babban a gaban gwamnonin shiyyar wajen ganin an yiwa tufkar hanci cin gaggawa.

Shugaban kungiyar gwamnonin na arewa ya cigaba da bayanin cewa a yanzu haka kungiyar na nazarin sahihan hanyoyin bunkasa  tattalin arzikin shiyyar, ta hanyar farfado da kamfanin raya yankin arewa NNDC, haka kuma yace suna kokarin bullo da hanyoyin saka jari a bangarorin tattalin arziki daban-daban da Allah ya horewa shiyyar.

A jawabin sa gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani yace hakika a yanzu an fara samo hanyar tabbatar da wanzuwa zaman lafiya a shiyyar arewa cin Najeriya, bisa samun hadin gwiwa da gwamantin tarayyar.

“ Gwamnatin tarayyar karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta nuna jajircewar ta wajen maganin ayyukan `Yan bindiga da masu satar mutane a shiyyar”

Akan batun `yan sandan jahohi kuwa, gwamnoni sun amince da bin tsare-tsaren ayyukan yan sandan jahohi har zuwa lokacin da al`ummar kasa zasu kammala muhawara akai.(Garba Abdullahi Bagwai)