logo

HAUSA

Mutane 24 sun mutu sanadiyyar ruftawar titi a lardin Guangdong na kasar Sin

2024-05-01 20:04:08 CMG Hausa

Hukumomi a birnin Meizhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, sun ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar ruftar wani bangare na wata babbar hanyar mota a birnin, ya karu zuwa 24, kana wasu mutane 30 kuma suna jinya a asibiti, amma jikkatar ba ta barazana ga rayuwarsu.

Lamarin ya auku ne da safiyar yau Laraba, inda ya rutsa da motoci 20. (Fa’iza Mustapha)