logo

HAUSA

Me ke kara jan hankalin tarin masu zuba jari zuwa ga kasar Sin ciki har da manyan kamfanonin kasa da kasa?

2024-05-01 08:03:51 CMG Hausa

Masharhanta da dama na alakanta karbuwar da kasar Sin ke kara samu ga sassa masu zuba jari, ciki har da manyan kamfanonin kasa da kasa da babbar kasuwar kasar, da ingancin hidimomin safarar kayayyaki, da tarin ma’aikata masu basira da kwararru da kyakkyawan fatan da ake yiwa ci gaban kasar ta fuskar kasuwanci.

Ko shakka babu, kasar Sin na kara jan hankulan masu zuba jari daga ketare, kamar yadda alkaluman hukumokin kasar ke bayyanawa. A baya bayan nan ma ma’aikatar cinikayyar kasar ta ce adadin sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka yiwa ajista, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2024 ya kai 12,000, karuwar da ta kai ta kaso 20.7 bisa dari kan na makamancin wannan lokaci na bara.

Kaza lika, a watannin baya bayan nan, kasar Sin ta kaddamar da sabbin manufofin kara bude kofa ga waje, wadanda ka iya karfafa gwiwar sassan kasa da kasa na su zuba jari a kasar a kamfanonin kirkire kirkiren fasahohi, duk da nufin saukakawa masu zuba jarin na waje hanyoyin shiga a dama da su a wannan babbar kasuwa.

Bisa sakamakon da kasar ta samu a fannonin raya tattalin arziki daban daban, da yawa daga cibiyoyin ketare sun daga hasashen su na bunkasar tattalin arzikin Sin. Inda kamfanin hada hadar kudade na “Goldman Sachs” ya daga hasashen sa na bunkasar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kaso 5 bisa dari a bana, sama da karuwar kaso 4.8 bisa dari da ya yi a baya. 

Bugu da kari, alkaluman kididdiga na ma’aikatar cinikayyar kasar Sin na watan Afirilu, sun nuna karuwar kashe kudade tsakanin Sinawa masu sayayya, musamman a bangaren manyan kayayyaki kamar su motocin hawa, da kayan amfanin yau da kullum na gida, da kayan kawata wuraren zama na katako, tun daga rubu’in farko na shekarar nan, yayin da fannonin ba da hidima su ma suka samu babban tagomashi a wannan wa’adi. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)