An yi gwajin tafiya cikin teku na jirgin ruwa mai dauke da jiragen saman yaki na uku na Sin
2024-05-01 16:28:52 CMG Hausa
Da safiyar yau Laraba, aka gudanar da gwajin tafiya karo na farko cikin teku, na babban jirgin ruwa mai dauke da jiragen saman yaki, irinsa na uku na kasar Sin, mai suna Fujian.
Bisa matakan kera babban jirgin ruwa mai dauke da jiragen saman yaki, dalilin gudanar da gwajin na yau shi ne, tantance inganci da amincin tsare-tsaren babban jirgin ruwan mai dauke da jiragen saman yaki na Fujian, kamar karfinsa na tafiya, da kuma tsarin aikin wutar lantarki.
Tun bayan fara amfani da shi a watan Yunin shekarar 2022 a cikin ruwa, ana ci gaba da gudanar da aikin kera babban jirgin kamar yadda aka tsara, kuma an kammala aikin gwajin ajiye jirgin a tashar ruwa da tantance kayayyakin aiki, sannan an cika sharuddan fasahar shiga teku domin yin gwaje-gwaje. (Safiyah Ma)