logo

HAUSA

Beijing: An Kafa Sansanin Ba Da Horo Kan Mu’amala Da Hadin Kai Ta Fuskar Ci Gaban Mata Na Duniya

2024-04-30 11:01:50 CMG Hausa

Jiya Litinin hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin, da hukumar hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar, sun kaddamar da sansanin ba da horo a fannin yin mu’amala, da hadin gwiwa ta fuskar ci gaban mata na kasa da kasa a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

An kafa sansanin ne domin shirya wa kasashe masu tasowa ayyukan da za su biya bukatunsu, kamar kyautata kwarewar mata, da ziyarar karatu tsakanin masana da manyan jami’ai a kasar Sin, da ba da horo da dai sauransu, a kokarin samar wa mata dandalin kyautata kansu, da kara azamar ci gabansu, da yin mu’amala da hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za a sa kaimi ga sha’anin mata na duniya.

An ruwaito cewa, hukumar hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin, za ta hada hannu da sassa daban daban a fannin kara karfin horas da mata, da gudanar da wasu kananan ayyuka managarta na kyautata jin dadin mata, da shigar da karin kudi, da ma’aikata don goyon bayan sansanin dake taka muhimmiyar rawa wajen kara azamar yin hadin gwiwa, da mu’amala, da kuma ba da horo tsakanin matan kasa da kasa. (Tasallan Yuan)