Hungary na sa ran ziyarar Xi za ta bude sabon babi a dangantakarta da Sin
2024-04-30 21:13:45 CMG Hausa
Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Mayu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai yi ziyarar aiki a kasashen Faransa da Serbia da Hungary.
Yayin wata tattaunawa a baya baya nan da kafar CMG, ministan harkokin wajen Hungary Szijjarto Peter, ya ce a bana Sin da Hungary za su cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya, kuma Hungary na sa ran ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar, za ta bude wani sabon babi a dangantakarta da Sin. (Fa’iza Mustapha)