logo

HAUSA

Dawud Jidda Jidda: Akwai damammakin kasuwanci da ilimi sosai a kasar Sin!

2024-04-30 15:32:41 CMG Hausa

Dawud Jidda Jidda, dan asalin birnin Maiduguri na jihar Bornon tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake harkokin kasuwanci a kasar Sin.

Dawud ya ce, lokacin da ya fara harkokin kasuwanci tare da Sinawa, ya karu sosai ta fuskar ilmomin da suka shafi saye da sayarwa, da kai kawon hajoji, gami da tafiyar da cinikayyar kasa da kasa.

Game da bikin baje-kolin hajojin da ake shigowa da su gami da wadanda ake fitarwa zuwa ketare na kasar Sin, wanda aka fi sani da suna “Canton Fair”, wanda a yanzu haka yake gudana a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kasar Sin, Dawud ya ce, kayayyakin zamani iri-iri, gami da damammakin kasuwanci da yawa, duk sun burge shi kwarai da gaske.

A karshe, malam Dawud, wanda ya bude kamfanin Dawjid International a nan kasar Sin, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suke sha’awar zuwa kasar Sin yin karatu ko kasuwanci, da su tashi tsaye don cin gajiyar damammakin da kasar Sin ke samarwa. (Murtala Zhang)