Tawagar jami’an wanzar da zaman lafiya ta Sin ta bayar da gudunmuwa ga DRC
2024-04-30 20:58:12 CMG Hausa
Tawagar jami’an kasar Sin dake cikin tawagar shirin wanzar da zaman lafiya na MDD (MONUSCO), ta bayar da gudunmuwar kayayyakin aikin injiniya da injuna da kayayyakin kiwon lafiya, ga gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC a jiya Litinin.
An gudanar da bikin mika kayayyakin ne a wajen birnin Bukavu, hedkwatar lardin South Kivu dake gabashin kasar. (Fa’iza Mustapha)