logo

HAUSA

Wasu kungiyoyin dake hakar ma`adanai ba bisa ka`ida ba a Najeriya sun dunkule wuri guda wajen samun lasisin gwamnati

2024-04-30 09:25:38 CMG Hausa

Ma’aikatar lura da harkokin ma`adanai a tarayyar Najeriya ta sanar cewa wasu kungiyoyi guda 70 da suke hakar ma`adanai ba tare da izini ba sun dunkule wuri guda, inda yanzu suka mallaki lasisin izinin hakar ma’adanai daga gwamnati.

Ministan ma’aikatar Mr Dele Alake ya tabbatar da hakan jiya Litinin yayin wani taron karawa juna sani na yini biyu da aka shiryawa manya da kananan ma’aikatan ma’aikatar a birnin Abuja. Ya ce, yanzu wadannan kungiyoyi za su biya haraji kai tsaye ne zuwa ga asusun gwamnatin tarayya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

 

Mr. Dele Alake ya yi kurarin cewa dukkan kungiyoyin da ba su yi kokarin mallakar lasisin izinin ci gaba da wannan sana’a ba, tabbas za su ci karo da fushin jami’an tsaron musamman da aka tanadar domin hukunta musu hakar ma’adanai ba tare da izini ba.

Ministan ya ce, har yanzu ma’aikatar tasa tana bin hanyar masalaha ga irin wadannan kungiyoyi, saboda ta lura wasun sun ba su da karfin da za su iya hada kan membobinsu wuri guda, amma ma’aikatar kamar yadda ya fada, a shirye take ta taimakawa irin wadannan kungiyoyi a wuraren da ya kamata domin tabbatar da ganin sun mallaki lasisin cikin sauki.

Mr. Dele Alake ya kuma ja kunne wadanda ba su nuna wani yunkuri na mallakar lasisin ba, cewar gwamnati tana da hanyoyin amfani da karfin doka wajen tilasta sus u yi hakan ko kuma su bar sana’ar gaba dayan ta.

“Za mu iya amfani da karfin jami’an tsaro a kan irin wadannan mutane, tuni ma dai muka fara daukar irin wannan mataki a kansu, domin ko a makon da ya gabata runudnar jami’an tsaro musamman da aka samar domin lura da wuraren hakar ma’adanai sun kama wasu mutane a Abuja da kuma jihar Nasarawa.” (Garba Abdullahi Bagwai)