logo

HAUSA

CMG ya kaddamar shirin musayar al’adun abinci na Sin da Faransa

2024-04-30 20:27:24 CMG Hausa

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyarar aiki a kasar Faransa a 'yan kwanaki masu zuwa, a yau Talata, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da hadin gwiwar ofishin jakadancin Faransa dake Sin, sun kaddamar da wani katafaren shirin musayar al’adun abinci na Sin da Faransa da aka yi wa lakabi da "Chinese French Chef King Competition" wato gasar girki ta Sin da Faransa.

Da yake gabatar da jawabi yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce a shirye CMG yake ya yi koyi da juna da abokansa na Faransa daga dukkan bangarorin rayuwa, tare da hada hannu da su domin kyautata makomar abotarsu. (Fa’iza Mustapha)