logo

HAUSA

Bankin Duniya ya alkawarta samar da lamuni mai rahusa ga kasashen Afirka

2024-04-30 11:01:49 CMG Hausa

Shugaban bankin duniya Ajay Banga, ya bayyana aniyar bankin na samar da lamuni mai rahusa, kuma mai wa’adin dogon lokacin biya ga kasashen Afirka, kana da yin aiki tare da gwamnatocin kasashen nahiyar wajen wanzar da ci gaban nahiyar.

Ajay Banga ya ce, sashen bankin mai lura da ci gaban kasa da kasa ko IDA, zai samar da kudaden gudanar da ayyukan dakile sauyin yanayi, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma manufofin rage fatara.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron shugabannin Afirka da sashen na IDA ya shirya a birnin Nairobin kasar Kenya a jiya Litinin, wanda aka yiwa lakabi da IDA21, Banga ya ce, "Dole ne mu yi amfani da damar dake akwai, wajen cimma gajiyar nahiyar Afirka. Wajibi ne nahiyar ta samu sauyi na gari."

A nasa jawabin kuwa, shugaban kasar Kenya William Ruto, kira ya yi da a kara adadin kudaden da sashen na IDA ke samarwa, daga dalar Amurka biliyan 93 a shekarar 2022 zuwa dala biliyan 120 a shekarar nan ta 2024.

Ruto ya ce, ya dace a shawo kan matsalar hauhawar bashin dake wuyan kasashen Afirka, mai nasaba da kalubale da dama dake addabar duniya, ta hanyar yin hadin gwiwa da hukumomi irin su IDA. (Saminu Alhassan)