Xi ya aike da sakon taya murna na ranar ‘yan kwadago ta kasa da kasa
2024-04-30 20:09:14 CMG Hausa
A jajibirin ranar ma’aikata ta kasa da kasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna da gaisuwa na ranar ga ma’aikata na kasar Sin.
Cikin sakon, Xi Jinping ya bayyana cewa, ma’aikatan kwadago suna aiki tukuru da kuma ba da gudummawa ba tare da son kai ba, inda suke taka muhimmiyar rawa wajen ingiza ci gaban JKS da ma kasar, da basira da kuma guminsu.(Safiyah Ma)